Min menu

Pages

Makaranta Hausa Film: Shirin Farko Dayake Koyar Da Jima'i Kwanciyar Aure

Makaranta Hausa Film
Makaranta Hausa Film

Makaranta Hausa Film: Shirin Farko Dayake Koyar Da Jima'i Kwanciyar Aure

Wani abin mamaki yana shirin faruwa a arewacin kasar Nigeria a masana'antar shirya fina finan Hausa wato Kannywood, A karon farko an samu wani mashiryin wasan kwaikwayo ya shirya wani film mai suna Makaranta Hausa Film wanda gaba daya acikin shirin ana koyar da yadda ake Jima'i ne wato kwanciyar aure

A tallan shirin Makaranta da aka nuna akan Youtube anga yadda wasan kwaikwayon yake nuna wata makaranta da 'yan mata da samari suna karatu akan sanin Kwanciyar Aure, Acikin tallan, zakaga da kuma jin kalamai na batsa wanda ba a saba ji ba a fina finan Hausa

Makaranta Hausa Film

Sai dai wannan shirin tun kafin fitowar sa yagamu da kalubale da kuma suka daga wajen mutane dadama musamman masu bibiyar shafukan sada zumunta, shugaban hukumar tace fina finai ta jahar Kano wato Isma'il Na'abba Afakallahu yasha alwashin bin duk wata hanya da doka tabasu dama don suga ba a nuna shirin Makaranta Hausa Film ba, kamar yadda yafada shirin babbar barazana ce ga tarbiyyar al'ummar arewacin Najeriya

Akwai dai fina finan Hausa da ake yawan zargin suna da tasiri wajen lalacewar tarbiyyar matasa wanda kuma 'yan fina finan Hausa sunsha musawa cewa shirya shiryen nasu basa bata tarbiyya, asalima su suna koyar da tarbiyyar ne

Sai dai idan za a fadi gaskiya shirin Makaranta wanda yake kusa da fitowa zai kawo babbar gudummawa wajen lalacewar tarbiyyar mutane a arewacin kasar Nigeria musamman matasa, yanzu dai mutane sun zuba ido domin suga za a fitar da Makaranta Hausa Film ko kuwa Isma'il Na'abba Afakallahu zai samu nasarar hanawa

Comments