Min menu

Pages

Idan saurayi ya kamu da kaunar budurwa sace ta yake ya kulleta a wannan kabilar..

 Idan saurayi ya kamu da kaunar budurwa sace ta yake ya kulleta a wannan kabilar..Kamar yadda kowa ya sani wannan duniyar ta tara abubuwa masu matukar yawa a cikinta saboda yadda take da girma.


Abubuwan data tara sun hadar da yawan mutane da kuma yawan kasashe sannan da kuma kabilu masu al'adu da yawa.


Wasu daga cikin kabilun suna gabatar da wasu irin al'adu wasu masu kyau da birgewa wasu kuma akasin haka musamman wajen neman aure da sauransu.


Yau cikin shirin namu zamu kawo muku labarin wata kabila ne wacce idan saurayi yaga budurwa tayi masa zai dauketa ne yaje ya kulleta.


Kamar yadda wasu kabilun suke su idan saurayi yaga budurwa wacce tayi masa zaije ne ya same ta ya bayyana mata yadda yake sonta idan ta amince shikenan sai suyi ta soyayya kafin daga baya kuma a shigar da maganar auren gurin manya.Kabilar Frafra da suke kasar Ghana su tasu dabi'ar ba haka take ba domin daga zarar saurayi yana son budurwa to kuwa zai sace ta ne yaje ya kulleta a gidansu sannan yasa mata tsaro yadda bazata iya guduwa ba.


Daga nan sai danginsa su samu goro da zabi da kuma taba sukai gidan su yarinyar a matsayin kayan an gani ana so, kuma anzo ne ayi maganar aure, wannan shine zai bawa iyayen yarinyar damar sanin wanda ya dauke musu yar tasu.


Sannan iyayen saurayin zasu gargadi iyayen yarinyar cewar saurayin zai yiwa diyarsu ciki matukar suka ki yadda da alkawarin auren yaran.


Bayan iyayen yarinya sun amince za a yanka raguna da karnuka da zabi harda talo talo a gidan su yarinyar a matsayin shidima ta biki.


Mu hadu daku a wani sabon shirinComments