Min menu

Pages

kowacce mace burinta ta samu na miji mai abubuwa 5 dinnankowacce mace burinta ta samu na miji mai abubuwa 5 dinnan Kasancewar kowacce mace tanada ra'ayi kuma tanada buri musamman bangaren zaben abokin rayuwa, ina nufin wanda zasu aura.


Hakan yasa mukai bincike muka zakulo muku wasu abubuwan da mata ke son suga wanda zasu aura yanada shi.


Duk da kasancewar ba kowanne na miji bane ke tara duka irin wadannan abubuwan amma dai mace ita kullum babban burinta ta samu na miji mai irin wadannan abubuwan.


Ilimi:- Kowacce mace nada burin ganin ta auri na miji mai ilimi ko kuma muce mai karatu bangaren boko dana addini.Kyau:- Kowacce mace nada burin auren na miji mai kyau ko kuma dan gayu.


Kudi:- Kusan yanzu kam duk wata mace tanada burin auren miji mai kudi domin idan mutum bashi da kudi ma wasu daga cikin yan mata basu cika sauraron sa ba.


Mai iya kalamai:- A yanzu lokaci ya canja mata sunada bukatar miji ko saurayi wanda ya iya kalamai na soyayya wanda kullum zai rika jefa musu kalamai iri iri na soyayya.


Mai gaskiya:- Anan kusan kowa haka yake tsakanin mata domin dukansu suna son mutum mai gaskiya.

Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da mata ke son samu gurin maza.

Comments