Min menu

Pages

Cututtukan da suke kama Al'aurar mata,wadan da suke hana mace jin dadi yayin saduwa da kuma jin zafi

Cututtukan da suke kama Al'aurar mata,wadan da suke hana mace jin dadi yayin saduwa da kuma jin zafi.Yau cikin shirin namu zamu zayyano muku wasu cututtuka ne da suke kama Al:aurar mata Dan haka muje cikin shirin

VAGINITIS : Wata cutace da mafiya yawan jama'a su na kiranta da Vaginal Infection sabida wannan matsalar ta na addabar gaban mace . Amma a Hausance a na kiranta da Ciwon Sanyin Mata.


Wannan cutar wasu kwayoyin cutar Bakteriya da Fungus da ke zaune acikin Gaban mace su su ke kawoshi.


A na Iya samun wannan ciwon a lokocin juna biyu (ciki) da shayarwa , haka kuma za a iya samun ciwon ta hanyar jima'i .


CAUSES OF VAGINITIS:

👇🏾


1- Bacteria Vaginosis : wannan wani kwayar cutace da ke rayuwa cikin farji, ya kan haddasa matsalar Sanyin mata .


2- Candidiasis : wannan wata kwayar cutace Wanda ta ke haddasa Sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cutar su na zama cikin farji kuma ba su cika cutarwa ba, wadannan kwayoyin cutar su na son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.


3- Trichomonas Vaginalis : wannan ita ce wacce ta ke yaduwa ta hanyar jima'i. Ita wannan kwayar cutar parasite ce ta ke kawoshi .


4- Irritation Vaginitis : ita wannan a na kiranta da Allergic , wassu abubuwan da jikin mutun bai daukesu ba, a na samunsa wajen amfanida kamar su condom, sabulu , ko maganin shafawa.


SIGN AND SYMPTOMS


1- Kumburin Farji

2- Canza Launin Farji zuwa Ja.

3- Kaikayin Farji

4- Warin Farji

5- Kurajen Farji

6- Zubar da Farin ruwa a Farji.

7- Jin Zafin Lokocin Jima'i

8- Zafin Fitsari.


PREVENTION OF VAGINITIS:

👇🏾

1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akwai wassu kwayoyin bakteriya wadanda ba sa cutarwa kuma su na da amfani , amfaninsu shine su na taimakawa wajen bayar kariya ga Farji , sai ka ga wasu matan su kan wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwan da a ke amfani da su wajen wanke farji ya kan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke Farji Da Sabulu da kuma wadansu abubuwa Wanda ba mu san Kansu ba.


2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants , wasu matan su kan bar wandonsu ya yi datti , Barin datti ko amfani pant masu datti ya kan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji.

A Tsaftace wanduna.


3- Cleaning Faeces : wajen wanke bahaya mafi yawan mata su kan dauki kwayar cutar da ta ke duburarsu zuwa Farji, wanda ba sa yi wa dubura illa amma su kan yiwa Farji illah.

 Shawara shine a fara wanke Farji kafin a wanke dubura.


4- Sharing of Underwear: amfani da pants na wasu , ta yiu wacce ku ke amfani da pants daya ta na da cutar Sanyi idan kin yi amfani da nata kema za ki iya dauka.

Sai a kiyaye.


5- Sexual intercourse : mutun yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji shawara itace adinga amfanida Condom lokocin saduwa.


Shawara Idan mace ta ga daya daga cikin wadannan alamomi da mu ka lissafa daga sama ta garzaya zuwa asibity domin agane me ya ke damunta kuma a bata maganin da ya dace da ita, domin wannan matsalar ba na kemis bane .


Allah ya kiyaye Allah kuma ya kara mana lafiya.


Domin bukatar magani 08137482786 muna jahar kano kasuwar kofar ruwa cikin tashar kuka @maijalalaini islamic chemist


Comments