Min menu

Pages

Abubuwa 4 idan kuna yi bazaku taba samun haihuwa ba

 Abubuwa 4 idan kuna yi bazaku taba samun haihuwa baBazaku taba samun haihuwa ba idan kuna aikata wadannan abubuwan

Akwai abubuwa da idan mutane suna aikatawa bincike ya nuna da wuya su iya samun haihuwa duk kuwa da cewar ita haihuwa daga Allah ce idan ya baka dole saika samu.

To amma akwai wasu abubuwa da yawan aikata su kan hana haihuwa dan haka zamu zayyano muku guda hudu daga cikinsu.


√ Istimna'i zinar hannu masu bincike kan ilimin sanin lafiyar dan adam sunce yawan aikata Istimna'i wato zinar hannu ko kuma biyawa kai bukata da hannu walau mace ko kuma na miji kan durkusar da kwayoyin halittar dan adam harma su kasance sunyi rauni wanda hakan zaisa kwayoyin halittar su kasa kinkisar junansu ba wanda hakan zaisa mutum ya gagara samun haihuwa.


√ Dora computer akan cinya:- Yawan dora computer akan cinya na tsawon lokaci kan hana haihuwa shima, misali ace mutum kullum yana aiki da computer kuma baya dorata a ko ina idan zaiyi aikin sai akan cinyarsa wannan zaisa duk wani dumi ko zafin dake jikin computer yana sauka a kan gabansa.

Wannan ma kan iya hana haihuwa inji masu binciken.

√ Yawan shan taba cigarette 🚬 yawan shan taba ma yana iya sawa mutum yaki haihuwa.

√ shan giya:- Bincike ya nuna shan giya kan dakusar da bangarori da dama na jikin dan Adam harma da bangaren daya shafi haihuwa.

Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da suke jawo rashin haihuwa.Comments