Min menu

Pages

Sani Garba SK Kannywood Jarumin Fina Finan Hausa Ya Rasu

Sani Garba SK Kannywood

Sani Garba SK Kannywood Jarumin Fina Finan Hausa Ya Rasu

Duk wani mai dai mamaci ne wata rana kamar yadda yau Allah yadauki ran Sani Garba SK Kannywood Jarumin Fina Finan Hausa wanda yashafe shekara da shekaru yana wannan sana'a, a baya dai an yayata mutuwar jarumin sai dai abokan sana'arsa sun fito sun karyata a waccan lokacin

Allahu Akbar yau dai Sani Garba Sk ka'ida tazo wanda jaruman kannywood su suka bayyana mutuwarsa a shafukan sada zumunta, kafin mutuwar jarumin yayi fama da doguwar rashin lafia wanda har sai da aka yada a kafafen sada zumunta ana nema masa kudin magani

Sani SK yashafe kusan shekara uku yana fama da rashin lafia sai dai bata hanashi ayyukan da yakeyi ba da farko, a cikin wannan shekara da muke ciki ne jiyar tasa tayi tsanani inda sai da yayi sama da sati biyar a asibiti

Sani Garba Sk yayi fama da Ciwon Siga ne wanda abokan sana'arsa suka bayyana cewa daga baya cewon sigan ya haifar masa da ciwon koda da kuma hawan jini, an fara masa wankin koda a ranar dazai rasu inji abokin aikinsa Abdul Amart

Sani Garba SK Biography

Sani garba sk dan asalin garin Kano ne a unguwar Zage wanda kuma kamar yadda BBC Hausa ta bayyana kafin yashiga harkar fina finan Hausa mai yabon Manzon Allah ne a kungiyar Usha'un Nabiyyu

Ya kwanta jinya a Asibitin Nasarawa da kuma Asibitin Murtala dake cikin birnin Kano, yanzu haka an tafi da gawar Sani Garba Sk Kannywood gida wanda gobe za ayi masa Sallah kamar yadda Addinin Muslunci yatadanar

Comments