Min menu

Pages

Mutumin da yayi shekaru 20 ba tare da yasha ruwa ba

 Mutumin da yayi shekaru 20 ba tare da yasha ruwa baKo kunsan wannan mutumin shine yayi shekaru 20 ba tare da yasha ruwa ba saboda wani dalili nasa?


Kowacce rana tana zuwa ne da abubuwa na mamaki kala daban dabam, idan kuna rayuwa da zaku hadu dasu su baku mamaki.


A yau munyi karo da wani mutum da yayi shekaru 20 ba tare da yasha ruwa ba.


Wani mutum ya bayyana yadda yayi shekaru 20 ba tare da yasha ruwa ba, ya fada a wata tattaunawa da sukai cewar ya daina shan ruwa ne kimanin shekaru ashirin kuma yana gabatar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali kamar sauran mutane.


To saidai bai bayyana dalilinsa na daina shan ruwan ba kawai dai yace ya daina ne ba tare da wani dalili ba.


Koda yake bada labarinsa yace da farko shi mai arziki ne kafin daga baya ayi masa sharri a kaishi gidan yari a kulle shi akan laifin da bai aikata ba.


Ruwa yanada matukar amfani ga rayuwa domin dashi wasu suke rayuwa amma shi wannan yana gabatar da rayuwarsa ne gaba daya ba tare da yasha ruwa ba.


Mutumin sunansa Karton Rastafari, dan kasar Burundi ne wanda yake zaune a wani kaunye.

Comments