Min menu

Pages

Mata a wannan kabilar basa auren mazaje sirara sai masu katon tumbi.

 Mata a wannan kabilar basa auren mazaje sirara sai masu katon tumbi.

 


A kabilar Bodi, iya girman tumbinka iya farin jininka a gun yan mata.


Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai.


A yau cikin shirin namu munzo muku ne da labarin wata kabila da matan cikinta sunfi so da kaunar maza masu katon tumbi.


A tsarin kabilar Bodi dake kasar Ethiopia, mazajen masu katon tumbi sune wadanda mata suka fi rububin dauka kuma suka fi so da kauna.


Domin a kabilar iya girman tumbinka shine yake nuna irin farin jininka a tsakanin 'yan matan garin.

Wannan yasa mazan garin suke bakin kokarinsu ganin sun karawa tumbinsu girma domin su samu yan matan da za suyi rububinsu.


Suna gauraya jini da madara, sannan su sha domin kara kiba da kuma kara girman tumbin nasu. 


'Yan Wannan kabila ta BODI suna zaune ne a wani dan karamin tsuburi da ake kira da Omo a kasar ta Ethiopia, kuma suna matukar alfahari da wannan al'ada tasu ta rainon tumbi.


Mu hadu daku a wani sabon shirin kudai ku ci gaba da kasancewa tare damu.



Comments