Min menu

Pages

Izzar so episode 70 - Mp4 download Bakori tv - Hd Movie

Izzar so episode 70 - Mp4 download Bakori tv - Hd MovieAkwai dalilin da yasa har yanzu shirin izzar so bai iso gurin masu kallo ba wannan yana zuwa ne saboda wasu dalilai.


Tun jiya da mutane masu bibiyar shirin suka duba tashar Bakori tv inda ake dora wannan shirin mai farin jini wato izzar so suka ga basu ganshi ba wasu suke ta fadar albarkacin bakinsu wasu sun fahimta cewa matsalar aka samu kamar yadda mai shirya shirin ya fada a wato Lawan Ahmad a wata sanarwa da yayi cikin Facebook page dinsa.


Wasu basu ji dadin faruwar hakan ba duk kuwa da cewa suma masu shirya film din basu ji dadin ba amma wasu da dama suna fada harda zage zage.


Hatta su masu shirya film din basu ji dadin rashin kawo shirin a lokacin da ya dace ba kuma basa son hakan ya kuma faruwa.


Duk da haka ana bewa masu kallon shirin hakuri akan cewa matsalar na'ura aka samu kuma anata kokari ganin an gyara abin nan bada dadewa ba.


Tun jiya ake kan aikin na'urar amma har yanzu dai ba'a samo kanta ba amma dai ana gyarawa wanda nan da wani lokacin za'a kawo muku shirin na izzar so episode 70 a tashar Bakori tv.


Dan haka kuyi hakuri masoya koda yaushe muna godiya kuma muna tare daku.

Comments