Min menu

Pages

Wasu birane a nahiyar Africa mafiya kyau da kawatuwa

 Wasu birane a nahiyar Africa mafiya kyau da kawatuwa


Duk lokacin da aka bukaci yin tambaya cewar mutum ya bayyana abu mai kyau kai tsaye abinda zai fara bayani shine yanayin yadda abin yake ta fuskar tsafta kwalliya, rashin hayaniya da kuma sauran abubuwa.


To kamar haka ne idan aka ce mutum yayi bayanin birni mafi kololuwa wajen kyau zaiyi duba ya zuwa wasu abubuwa da birnin yake dashi kamar kyawun yanayin garin, kyawun titina kyawun gine gine, tsaftaceccen ruwa da kuma haske da dai sauransu.


To yau cikin wannan shirin zamu kawo muku bayanin wasu birane mafiya kyau wanda suka kure matuka a nahiyar Africa dan haka muje ga sunan wadannan biranen.


1. Cape Town dake kasar south Africa



Wannan wani birni ne daya hadu matuka wanda ya kure wajen kyawun abubuwa da suka hadar da gine gine da manyan titina da sauransu.


2. Tunis na kasar Tunisia



Birnin Tunis ya zamto makura a kasar Tunisia gaba daya kuma shine na biyu wajen kyawu kamar yadda bincike ya nuna.


3. Johannesburg South Africa



Cikin kasar south Africa ta ciri tuta domin ta tara birane mafiya kyau a nahiyar Africa baki daya.

Saboda tsarin yanayin garin na Johannesburg ya zamto birni na uku wajen kyau a nahiyar African.


4. Stone Town dake kasar  Zanzibar



Wannan ma wani hadadden burni ne na gani a fada mai dauke da abubuwa na birgewa da debe kewa.



5. Bahir Dar Ethiopia



Duk cikin kasar Ethiopia ana ji da wannan birnin saboda yadda ya kawatu duk da kasancewar ba shine babban birnin kasar ba amma dai yanada zubi da kuma tsari.

6. Cairo Egypt



Koda yake duk wanda yake tafiya har yawonsa yaje wannan birnin na Cairo shida kansa zai bada labarin yadda birnin ya hadu da abubuwa kala kala na kawa da ado.

7. Luanda Angola



Birnin Luanda hadadden birni mai kyawun fasali kenan, haka duk wadanda suka ziyarci birnin suke fada saboda ado da kuma launin yanayin birnin yake.

8. Agadir Morocco



Birnin Agadir dake Morocco birni ne makura a nahiyar Africa baki daya duk da kasancewar bai zamo birni mafi kololuwa ba wajen kawatuwa amma dai yanada kyau da fasali.

9. Abuja Nigeria



Idan kaje Abuja dauka za kayi bama a nahiyar Africa kake ba baki daya saboda yadda aka gina garin aka kawatashi, sannan akwai yanayi mai kyau ga dadi ta inda indai mutum yaje birnin zaiji tamkar wata kasar yake a cikin turai.


 10. Nairobi Kenya



Nairobi Kenya birnin tsafta da kyau kenan, sannan birnin mata.


Nairobi birni ne daya kawatu da manyan gine gine da tituna da sauran abubuwa.

Comments