Min menu

Pages

Wanda yafi kowa kazanta da datti a Duniya

 Wanda yafi kowa kazanta da datti Duniya.Amoo Hadji

Wannan mutumin shine ya shafe tsawon shekaru 67 ba tare da yayi wanka ba.An bayyana Amoo hadji a matsayin mutumin da yafi kowanne mutum kazanta da kuma rashin tsafta domin shine yayi shekaru 67 ba tare da yayi wanka ba.


Baya wanka ko kadan sannan baya yarda ya zubawa jikinsa ruwa domin yace duk ranar da yayi wanka to zai kamu da cuta dan haka babu ruwansa da wanka ko kadan.


Amoo hadji dan asalin kasar Iran ne dan cikin wani kauye da ake kiransa da Dejgah, sannan bashi da wani abinci da yafi so da kuma kauna kamar rubabben naman dabbobi musamman ma na alade.


Sannan yana  yin shaye shaye amma bana taba ba yana samun kashin dabbobi ne ya hada da gashinsu guri guda ya kunna wuta a cikin wani abu me kama dana lufe yana zuga kamar yana shan taba cigarette.


Tun Amoo hadji yana karamin matashi ya zabi ya kebance kansa daga mutane dan haka yayi damara ya dauki sulke ya daura a jikinsa bawai dan yayi yaki ba saidan ya kare kansa daga tsananin sanyi, sannan ya tona wani rami kamar kabari wanda idan ta raya masa sai ya shiga ciki ya kwanta.


Idan ka kusanci inda yake banda wari da doyi babu abinda yake tashi sannan idan yana magana har wani tururi mai cike da karni ne yake fita daga baki da hancinsa.Comments