Min menu

Pages

Matar da tafi kowacce mace muni a Duniya

 Matar da tafi kowacce mace muni a Duniya



Kamar yadda abubuwa ke kasancewa, za kuga kowanne jinsi akwai abokinsa. Ina nufin idan aka samu mace to akwai na miji, haka kuma idan aka samu akwai to dole babu ce kishiyarta, haka zalika idan ance akwai yunwa to za'a samu akwai koshi.


Dan haka duk inda akai bayanin kyau dole za'a samu muni.

                           Julia Pastrana



To yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da labarin wata mata wacce tarihi ya nuna tafi kowacce mace muni a Duniya.


A cikin duniyar nan da muke rayuwa tana cike ne da abubuwa na ban mamaki, domin abubuwa sun faru mafiya mamaki da suka fice a baya yayinda wasu kuma suke kan faruwa a yanzu.


Wasu mutanen an haife su tare da abubuwan mamaki da kuma baiwa kala kala wanda take iya sanyawa su zamo wasu mutane su shahara sosai a duniya a wannan zamanin da suke wasu kuma bayan sun mutu.


A cikin irin wadannan mutanen akwai wata mata me suna Julia Pastrana wacce aka haifeta a shekarar dubu daya da dari takwas da talatin da hudu a kasar mexico.


An haifeta da wasu abubuwa na ban mamaki wanda suka mayar da ita tai suna bayan ta mutu.


Da mummunar mace me gemu aka fi saninta a wannan lokacin, domin duk da kasancewarta mummuna ta gaban kwatance har gemu ne da ita wanda ya kara mata muni sosai da sosai.


Matar bata da kyau ko kadan domin har cewa ake tafi kama da namun dawa saboda yadda yanayinta yake da yadda mukamukinta suke da yanayin idanunta masu bada tsoro.


Wasu ma cewa suke ya kamata ta koma jeji tana rayuwa da sauran dabbobi yafi mata.

 Amma daga karshe wani dan kasar america ne ya aureta mai suna theode lent bawai saboda soyayya ba saidan kudi dan haka ya aureta domin ya nunawa duniya muninta wanda yasan a karshe zai samu kudi da ita.


Daga karshe ta mutu a shekarar dubu daya da dari takwas da sittin.


Mutuwarta tazo ne bayan ta haifi wani yaro mai matukar kama da ita sak! To amma shima bai jima ba ya mutu saboda wata cuta da yazo da ita.


Bayan ta mutu sai mijin nata ya rika daukar gawarta yana kaiwa kasashe yana nunawa domin ya samu kudi 


Daga karshe kafin a binneta saida aka kaita har jami'ar kasar Norway a shekarar 2013.











Comments