Min menu

Pages

Idan matar mutum tanada ciki dole saiya goyeta yabi takan garwashin wuta da ita saboda wannan dalilin

 Idan matar mutum tanada ciki dole saiya goyeta yabi takan garwashin wuta da ita saboda wannan dalilinAddinai da al'adu sunada yawa a wannan duniyar, wasu sun taso sunga ana gabatar da abubuwa na mamaki cikin kabilarsu wasu kuma saidai a basu labarin cewa anyi wata al'ada a baya kafin a haifesu.


Bayan haka kowacce al'ada sunada wani abu da suka rika a matsayin canfi wanda idan suka aikata shi zasu iya samun nasara a abinda suke nema.


Wannan yawan canfi da tsafe tsafen ya yawaita sosai cikin al'umma tun a farkon marra har zuwa yanzu.


Idan mutum yana zagaya duniya zaiga kabilu masu al'adu na ban mamaki wanda suke da matukar yawa wasu sukan bada mamaki wasu kuma saidai su bada haushi.


A yau cikin shirin namu munzo muku ne da wata al'ada a kasar China inda dole idan matar mutum tanada ciki dole saiya goyeta yabi takan garwashin wuta yayi tafiya mai nisa da ita.

Hakan shine zaisa ya nunawa mutane yadda yake tsakanin kaunarta kuma zai iya bata kariya a koda wanne lokaci.


Sannan kuma hakan da yayi na zagawa da ita kafarsa ba takalmi akan garwashin wuta shine zaisa a haifi yaron cikin kwanciyar hankali ba tare taji zafi ko kuma ta shiga wani hali yayin haihuwar ba, kuma jaririn zai kasance cikin koshin lafiya kuma zaiyi jarumta sosai.Comments