Min menu

Pages

Farashin Man Fetur zai iya komawa N340 A Cikin 2022- NNPC

Farashin Man Fetur zai iya komawa N340 A Cikin 2022- NNPC



Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari ya ce ak wai yiwuwar farashin man fetur ya kai N340 a shekarar 2022.


Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya na watan Nuwamba a Abuja ranar Talata.


Ya ce babu makawa za a cire tallafin mai a cikin shekarar mai zuwa, kamar yadda doka ta tanada.


“Babu wata doka da za ta tanadi ci gaba da biyan tallafin mai, amma na tabbatar za ku yaba wa tsare-tsaren da gwamnati za ta bullo da su don jin dadin jama’a, da nufin ganin talakawa ba su sha wahala ba,” inji shi.


A kan batun hauhawar farashin iskar gas kuwa, Shugaban na NNPC ya alakanta hakan da tsanantar bukatar yawan makamashin a fadin duniya, inda ya ce yanzu haka kasashe da dama na fuskantar karancinsa.


Mele Kyari ya ce farashin na yin tashin gwauron zabo ne saboda babu tallafin gwamnati a cikinsa, sabanin a man fetur.


Sai dai ya ce NNPC na aiki tukuru wajen ganin ya samar da wadataccen makamashin na iskar gas, kamar yadda aminiya ta ruwaito.

Comments