Min menu

Pages

Umaru Danjuma (Kasagi) Tsohon Marubuci Kuma Dan Wasan Hausa Ya Rasu

kasagi
Umaru Danjuma (Kasagi)

Allah yayiwa shahararren marubucin labarai kuma dan wasan Alhaji Umaru Danjuma (Kasagi) rasuwa ranar 29 ga watan 10, 2021. Kasagi dai ainihin dan jahar Katsina ne kuma acan Allah yayi masa rasuwa a ranar Juma,a.

Marigayi Kasagi ya shahara sosai wajen rubutu da kuma wasan kwaikwayo, za a iya cewa sune ainihin 'yan film din Hausa wanda suka dasa tushen fina finan Hausa a arewacin kasar Nigeria, Kasagi ya rasu yana da shekara 71 a duniya wato an haifeshi a shekarar 1950.

Alhaji Umaru Danjuma Kasagi ya rasu yana da 'ya 'ya 13 da kuma matan aure guda biyu, kuma marigayin yataba karatu a kasar Ingila domin koyon yadda ake shirya fina finai.

Kasagi a hirar sa da BBC Hausa kafin rasuwarsa ya bayyana cewa yasamu kyatuttaka a lokacin dayake zamaninsa na wasan kwaikwayo, kwanaki dai sai da aka yayata rasuwa kasagi wanda daga baya dansa ya fito ya karyata

Yanzu dai Allah yayiwa Alhaji Umaru Danjuma (Kasagi), sai dai muce Allah yajikansa da rahama.

Comments