Min menu

Pages

Izzar so da kuma dalilin fara yin shirin

  Izzar so da kuma dalilin fara yin shirin



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu?




Yau za muyi dan tsokaci akan shirin film din izzar so da kuma dalilin fara yin shirin daga gare mu har yadda ya fara zuwa gurin masu kallo.




Da farko kafin muyi nisa cikin tafiyar zan danyi tsokaci ga tarin mutanen da suke yawan yin korafi yanzu haka akan shirin izzar so da ake kan nunawa a channel din bakori tv.




Wasu suna yawan cewa shirin yana yin kadan wato tsawonsa baya zuwa da yawa kamar yadda suke so sannan kuma kyawunsa ya ragu ba kamar da farko ba.




To magana ta gaskiya shi dama shiri mai dogon zango haka yake dole idan ana tafiya za'a zo gurin da bazai yiwa masu kallo dadi ba domin kamar tafiya ce mutum yake yi a cikin mota akwai inda hanya take da kyau da dadin tafiya akwai kuma inda sai a hankali amma idan aka bi a sannu sai aga an sauka lafiya an isa inda ake so aje.




To kamar haka shirin yake gurin da kuke cewa bashi da kyau to ku dauka itace hanyar da bata da kyau in kuna tafiya kuma da sannu za'a zo inda zai birgeku fiye dana baya kudai abinda muke so daku kuyi hakuri kuci gaba da kallon shirin har zuwa gurinda zaku tabbatar da cewa munyi abinda ya dace.




Sannan batun tsayin shirin izzar so da kuke yin magana idan kun tuna a farko duka duka minutes nawa muke kawo muku? Idan kukai duba dana yanzu zaku ga mun kara tsayinsa dan haka kuyi hakuri zamu kuma dubawa.




  Dalilin da yasa muka shirya izzar so



Kusan kome dan adam zaiyi dole akwai manufa dan haka muma munada manufar da yasa muka fara kawo shirin, manufar kuwa ita ce mu nuna tasirin yin gaskiya a cikin kowanne abu da dan adam zaiyi a rayuwarsa, sannan da kuma yawaita addu'a da garkuwar da take sanyawa duk wani mai yinta.




Sannan mun nuna cewa duk lokacinda mutum ya nuna zaiyi wani abu mai kyau cikin mutane dole zai samu tarin kalubale wanda in mutum ya tsinci kansa irin wannan gurin abinda ake so yayi shine ya yawaita addu'a tare da hakuri.




Bissalam.

Comments