Min menu

Pages

Dan shekara 24 ya yiwa kannensa mata 3 ciki a jahar Legas

Dan shekara 24 ya yiwa kannensa mata 3 ciki a jahar Legas Wani matashi da aka sakaya sunansa mai shekaru 24 ya yiwa kannensa mata 3 ciki a jihar Legas. Uwar yaran ta bayyana cewar, mahaifin yaran baya zama a gari yayin da yake tafiya fatauci, daga bisani itama ta bude shago take kasuwanci.


Matar ta bayyana cewar, suna barin yaran nasu hudu a gida, inda babba yake da shekaru 24 yayin da 'yar autarsu take da shekaru 16, sai dai yayin da yaran ke zaune su kadai a gida suna kallon finafinan.


Matar ta fadi cewar, yaran sun shaida mata a yayin da suke kallon finafinai ne suka fara ganin fim din batsa tare, inda basu yi aune ba suka fara taba junansu.


Da daya daga cikin yaran tayi korafin fama da laulayi, an kaita asibiti inda aka yi gwaji aka gano tana da juna biyu, daga nan labarin ya fasu inda aka yiwa sauran yaran gwaji kuma aka gano suna dauke da juna biyu.Comments