Min menu

Pages

Yanzu harkar film bazata iya rikemu ba mu mata dole sai muna hadawa da yan dabaru

 Yanzu harkar film bazata iya rikemu ba mu mata dole sai muna hadawa da yan dabaru inji wata jarumaA dai dai lokacin da a ke ganin harkar fim tana Kara ci gaba tana bunkasa, sai ga shi jaruma kuma Furodusa a masana’antar ta na kira da abokan sana’ar ta, da su gane lokaci ya yi da harkar fim kadai ba za ta rike su ba, musamman ma dai jarumai mata.


Hakan ne ma yasa ta yi kira a gare su da su rinka hada wa da wasu sana’o’in ko kuma kasuwanci, kamar yadda ta ke a yanzu a matsayin yar fim, kuma babbar yar kasuwa.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, ya yin da yake mata tambaya a kan yadda a yanzu ba a cika ganin ta a cikin harkar fim din ba, inda ta ke cewa.


“Gaskiya a yanzu ban dade yin fim ba, Amma ko da an gayyace ni, a yanzu ba ni da lokaci, saboda harkokin kasuwancin da na ke yi na zuwa wasu kasashe sayen kaya, kuma wani lokacin ko da ina gari ba to yanayin kasuwancin ba zai ba ni damar na je fim ba, idan an gayyace ni.” Inji ta.
“Shi ya sa ko da an kawo mun fim to na kan ce ina da karancin lokaci, don kada na karbi fim din ya zama lokacin da za a fita aikin ba na gari, ko kuma ya kasance ina garin harkar kasuwancin nawa ya Hana ni zuwa, to ka ga sai mutum ya ga na bata masa Lokaci, don haka ba na karbar aiki.” a cewar ta.


“Amma dai idan na shirya nawa zan yi kamar yadda na ke zuba kudi na ke yin furodusin fim, to ka ga na san lokacin da zan ware don gudanar da aikin, kuma idan na ga babu lokacin sai na Kara lokacin, ka ga daman nawa ne ba na wani ba, shi ya sa a yanzu idan ba fim Dina ba ne to zai yi wuya na samu lokacin da zan je aikin wani. Wannan ce ta sa ba a gani na a fina-finan da a ke yi a yanzu. ”


Da muka yi mata tambaya a kan ko wacce shawara za ta bai wa abokan sana’ar ta ‘yan fim musamman mata?


Sai ta ce” To shawarar da zan ba su ita ce. Lokaci ya yi da za su gane harkar fim kadai ba za ta rike su ba” inji Sapna


“Domin kuwa suna cikin fim din za su yi aure, Kuma idan sun yi aure ba za su ci gaba da fim ba, don haka su raba kafa su rinka hadawa da wata sana’ar ko kasuwanci, ta yadda ko sun yi aure za su ci gaba da yin kasuwancin su. Wannan shi ne zai zama mafita a gare su. ” kamar yadda Sapna ta bayyana.Comments