Min menu

Pages

RIBAR ME DR AHMAD GUMI YAKE NEMA IDAN YA HADA KAI DA 'YAN TA'ADDA?

 RIBAR ME DR AHMAD GUMI YAKE NEMA IDAN YA HADA KAI DA 'YAN TA'ADDA?



Kamar yadda nayi alkawari a karshen rubutun da nayi mai taken ALAKAR SHEIKH DR AHMAD GUMI DA MASU GARKUWA DA MUTANE cewa zanyi bayani akan kuskure guda daya da Dr Ahmad Gumi yayi akan batun sulhu a Zamfara


Akwai mutanen da bayanai na kawai suke karantawa su yanke min hukunci ba tare da sun fahimta ba, wasu ma taken rubutun kawai suke karantawa, wasu kuma mahassada ne da suke jin haushin rubutuna a kafar sadarwa, amma ba yadda suka iya dani, domin har yanzu Allah bai halicci mutumin da zanji shakkarsa naki bayyana ra'ayi da fahimtata ba a rayuwa, zagi kuma kaimi da karfin gwiwa yake kara min


Kafin Sheikh Dr Ahmad Gumi (H) ya tsunduma kansa a harkan neman sulhu tsakanin barayin daji masu garkuwa da mutane da Gwamnati, Maigirma Gwamnan Zamfara Matawalle yayi nisa a cikin neman sulhun, sai dai shima Gwamnan ya hadu da cikas na rashin samun hadin kai da goyon baya daga Gwamnatin tarayya


An kai matsayin da a Zamfara jami'in tsaro bai isa ya kama mai garkuwa da mutum ya hukunta bashi ba, gaba daya ma sai da Gwamnan Zamfara ya hana jami'an tsaro operation da ya shafi Anti-kidnapping a fadin jihar Zamfara, ya soke 'yan banga da mafarauta, yayi haka cikin matakan da ya dauka na neman sulhu da barayin


Ba da jimawa ba, an kai matakin da aka zargi Gwamnan Zamfara da kulla alaka na ta'addanci da masu garkuwa da mutane a Zamfara, saboda ya hana jami'an tsaro suyi abinda ya dace, har wasu na cewa masu garkuwa da mutanen yaransa ne, shi yake saka su, ana cikin wannan yanayi sai Sheikh Dr Ahmad Gumi ya shigo cikin harkan neman sulhu


Gwamnan Zamfara yayi ta kokarin sulhu da barayin ba tare sa hannun Gwamnatin tarayya ba, ga kuma banbancin jam'iyyar siyasa dake tsakaninsa da Gwamnatin tarayya kafin ya dawo APC


Bayan tafiya tayi tafiya, Gwamnan Zamfara ya fahimci akwai maciya amana daga cikin masu rike da mukaman gargajiya a jihar, ya sauke su daga mukamansu, wasu aka kamasu suna tsare har yanzu, amma duk da wannan matakai da Gwamnan ya dauka baiyi tasiri ba, barayin sun zafafa hari da satar mutane


Gwamnan Zamfara sai ya ajiye batun sulhu, ya canza jam'iyyar siyasa, ya dawo APC, ya shirya damarar yaki da barayin, ya roki Gwamnatin tarayya ta dauke network da wasu matakai da ya bi domin hakan ya bawa sojoji damar yaki da barayin tunda sunki ayi sulhu, wato Gwamna ya ajiye batun sulhu ya rungumi batun yaki gaba da gaba


A babi na adalci, tunda yanzu Gwamna ya ajiye sulhu yace a yaki barayin, to ina wadanda a baya sukace Gwamnan yana samun kason sa daga masu garkuwa da mutane? Yanzu dai baku da ta cewa, sai ku nemi yafiyarsa.


Rayuwa kowa yana da tasa fahimtar da dabaru, zai iya faruwa hanyoyin da nake ganin za'abi domin ayi sulhu yasha banban da naka, don haka dole sai munyi juna uzuri, masifane yazo mana, an rikice an kasa samun mafita, amma a zargi wannan a zargi wancan bai dace ba, bata lokaci ne


Duk abinda ya kamata Gwamna Zamfara ya yiwa barayin daji ya musu, babu wani mataki da ya rage masa sama da ya bar jami'an tsaro su yake su


Karkashin wannan nake cewa idan akwai kuskuren da Dr Ahmad Gumi yayi to bai wuce cewa da yayi sojoji su dena ruwan wuta akan barayin jeji na jihar Zamfara ba, Malam ya fahimci cewa tunda barayin sunki yadda ayi sulhu su ajiye makami a bar jami'an tsaro suyi abinda ya dace kawai


Idan kuma a wani gari ne da ba Zamfara ba Malam Ahmad Gumi yake son ayi sulhu tabbas baiyi kuskure ba, saboda mun yadda da sulhu, munyi imani da abinda Allah Ya fada mana a Qur'ani cewa sulhu alkhairi ne, duk wani dan bindiga da bai yadda ayi sulhu ba mu su Datti Assalafiy muna goyon bayan a yakeshi kowaye


Amma duk wanda zaice Dr Ahmad Gumi yana jin dadi barayin daji suna garkuwa da mutane to bai masa adalci ba, kuma bai fahimci manufofinsa ba, kuma zamu cigaba da kalubalantar duk wanda yace Malam yana goyon bayan garkuwa da mutane wato ta'addanci


Yaa Allah Ka tsare mana rayuwar Malam Ahmad Gumi

Yaa Allah Ka shiryar da masu ta'addanci, Ka taimaki jami'an tsaro akan wadanda ba zasu shiryu ba Amin

Comments