Min menu

Pages

Wani dalili yasa Kotu ta umarci Hisbah a Jigawa ta ɗaura wa Khadijat da Hafsat aure duk da mahaifinsu ya ki amincewa

Wani dalili yasa Kotu ta umarci Hisbah a Jigawa ta ɗaura wa Khadijat da Hafsat aure duk da mahaifinsu ya ki amincewaKotu a karamar hukumar Hadejia jihar Jigawa ta yanke hukuncin a ɗaura wa wasu mata biyu aure duk da mahaifinsu ya ki amincewa da maneman da suka gabatar masa su na son su da aure.


Kafin kotu ta yanke wannan hukunci sai da ta baiwa mahaifin ƴan matan Abdullahi Malammadori kwanaki 30 ya aurar da ‘ya’yan na sa Khadijat da Hafsat Abdullahi amma ya yi bijire wa wannan umarni.


Khadijat da Hafsat sun ɗara shekaru 30 a duniya kuma basu taɓa yin aure ba.


Da Malammadori ya bijire wa umurin kotu sai kotun ta umurci hukumar Hisbah na jihar ta daura wa wadannan mata aure da maneman da suka gabatar.


Gidauniyar ‘Hadejia Women Foundation for Orphans and Vulnerable Children’ ce ta kai karar Malammadori kotu bayan ya ki amincewa da maneman da ‘ya’yan sa suka gabatar.


Shugaban gidauniyar Fatima Kailani ta bayyana cewa sun daɗe suna kai ruwa rana kan wannan batu amma Malammadori ya ki amincewa.


“Bayan ƙin amincewa da maneman da ‘ya’yan sa suka gabatar masa, shi kuma Malammadori bai fito musu da wanda shi suka kwanta masa a rai ya aura musu ba.


A wurin daurin auren da hukumar Hisbah ta shirya shugaban hukumar Ibrahim Dahiru ya ce an ɗaura wa Khadijat da Hafsat aure bayan maneman Sadiq Abdulruf da Abubakar Yusuf kowanen sun ya biya sadakin Naira 50,000 lakadan.


Hisbah ta daura wa wadannan mutane aure a ofishin ta dake garin Dutse, jihar Jigawa.


 Premium Times Hausa

Comments