Min menu

Pages

Majalisa Ta Bai Wa Ganduje Sa’o’i 48 Kan Ya Tsige Shugaban Hukumar Haraji Na Kano, AbduRazak Salihi

 Majalisa Ta Bai Wa Ganduje Sa’o’i 48 Kan Ya Tsige Shugaban Hukumar Haraji Na Kano, AbduRazak SalihiMajalisar Dokokin Jihar Kano ta bai wa Gwamna Umar Abdullahi Ganduje wa’adin sa’o’i 48 kan ya tsige Shugaban Hukumar Tara Haraji na Jihar, AbduRazak Salihi, daga muƙaminsa bisa laifin saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma rashin girmama majalisar da ya yi


Bayanai sun nuna Salihi ya ƙi bayyana wa Majalisar matsayin harajin da hukumarsa ta tara wa jihar duk da buƙatar hakan da Majalisar ta nuna masa, maimakon haka sai ya rubuta rahoto kan harajin tare da miƙa shi ga gwamnati ta hannun Babban Sakataren Hukumar Kula da Filaye ta jihar.


Kazalika, Majalisar ta hannun shugabanta Engr. Hamisu Chidari, ta nuna ɓacin ranta ga Salihi bisa yadda ya shirga wa ‘yan majalisar ƙarya duk da majalisar ta buƙaci da ya bayyana a gabanta.


Haka nan, Majalisar ta zargi shugaban hukumar harajin da rage wani harajin ‘yancin kasuwar fetur masu zaman kansu (IPMAN) daga N250 zuwa N100 wanda a cewarta hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa.


Yayin zamansu a ranar Talata, ‘yan majalisar sun nuna fushinsu tare da bayyana rashin gamsuwarsu dangane da ayyukan shugaban hukumar tara harajin wajen tara harajin jihar, da kuma rashin sanin makamar aiki da suka ce Salihi na fama da shi.


Chidari ya ce majalisar ta amince ta kafa kwamiti na mutum takwas wanda zai binciki koma bayan da aka samu game da harajin jihar Kano.


Salihi wanda aka gan shi yana kyarma a gaban ‘yan majalisar, ya kasa gabatar wa Majalisar da ƙwararan hujjoji kan dalilin da ya sa ya ƙetare Majalisar wajen miƙa wa gwamnati rahoton da ya shafi ayyukan hukumarsa.


Shugaban Kwamitin Majalisar Kan Sha’anin Kuɗi, Magaji Dahiru Zarewa, shi ne wanda zai jagoranci kwamitin da zai binciki Salihi.

Comments