Min menu

Pages

Kuyi gaggawar goge wadannan apps din idan har kuna dasu a wayoyinku..

 Kuyi gaggawar goge wadannan apps din idan har kuna dasu a wayoyinku..Assalamu alaikum yan uwa da fatan kuna lafiya.


A yau munzo muku da wasu apps wanda ake amfani dasu wajen cuta da kuma satar bayanai na mutum matukar akwai daya daga cikin application dinnan a cikin wayarsa..Wasu suna dora apps ne a wayarsu kawai idan sun san wani dan amfani da apps din yake dashi ba tare da suna duba da menene rashin amfaninsa a garesu ba.To dan haka akwai wasu apps da muka zo muku dasu wanda bincike ya nuna ana amfani dasu wajen nadar bayanan mutum matukar suna cikin wayarsa kama daga kan abinda ya shafi harkar banki wato asusun ajiyar kudade dadai sauran wasu bayanai masu matukar amfani ga mutum.


Harkers ko kuma nace masu satar bayanai suna amfani wajen tura abubuwan su cikin wadannan apps din domin dibar bayanai na jama'a musamman bangaren banki dan haka kuyi saurin kawar da wadannan apps din cikin wayoyin ku.Wadannan sune jerin Apps din da za kuyi hankali dasu ko kuma idan kuna dasu kuyi saurin goge su.


• Cake VPN ( com.lazycoder.cakevpns)


• Music player (com.revosleap.samplemusicplayers)


• BeatPlayer (com.crrl.beatplayers)


• QRecorder (com.record.callvoicerecorder)


• eVPN (com.abcd.evpnfree)


• QR/Barcode scanner MAX (com.bezrukd.qrbarcode)


• tooltipnatorlabrary (com.mistergrizzlys.canscanpro)


Ina shawartarku idan da hali duk wanda suke da irin wadannan app din a wayarsu suyi saurin goge su sannan suyi kokarin sake tsaro na wayoyinsu ma'ana su sake password a duk wasu bayanansu.


Mun gode

 Jerin wayoyin android da WhatsApp zai daina amfani akan su.

Comments