Min menu

Pages

Hanyar da zaku samu dollar dari cikin dan kankanin lokaci

 Hanyar da zaku samu dollar dari cikin dan kankanin lokaciA matsayin ku na yan Nigeria kuma matasa ko kunsan akwai hanyar da zaku bi ku hada kudi kimanin dollar 100 tare da wayoyin da kuke amfani dasu a dan karamin lokaci?


Wasu abin zai basu mamaki amma fa ba wani abin mamaki bane domin idan kuka fara harkar zaku tabbatar da maganar da nake fada muku..


Mutane suna yawan tambayar mu cewar ya za suyi suna samun kudi, a internet wasu kasancewarsu yan makaranta ne wasu kuma yan mata dake zaune a gida basu da sana'a wasu kuma matan aure ne wanda suke zaune a gida basu da abinda suke yana kawo musu kudi wannan yasa muka zabi mu sanar daku wasu hanyoyi da zaku bi wanda zaku samu kudi sosai da sosai.


Mutanen mu an riga an barmu a baya gaba daya musamman mu yan Arewa saboda bamu iya yin komai da wayoyin hannunmu su kawo mana kudi ba munfi kwarewa muyi shira kawai da yan mata ko kuma da samari, mun manta cewar da wayar da muke wannan ba karamin kudi zamu hada ba da mun maida hankali.


Shine yasa wasu yan kudu ko kuma yan wata kasar sukai mana fintinkau wajen samun kudi domin za kuga yara kanana suna hawa manyan motoci tare da gina gidaje masu tsada, wanda da ace za kuyi bincike ku samu ta inda wadannan suke samun kudaden su to za kuga da wayoyin hannunsu ne.


Sannan bayan wannan mu mutanen mu basa yin bincike suna gano wacce hanyar ya kamata su bi domin samun kudi suna kwance akan gado eh akan gado mana, na fadi wannan maganar ne domin na zaburar da abokaina matasa maza da mata cewar ana samun kudi da wayar hannu koda kuwa mutum yana kwance ne akan gado indai wayarsa na hannunsa.


To dan haka wannan rubutun kamar nuna hanya ne gareku matasa hanyar da zaku samu kudi cikin sauki da wayoyin hannunku.


Jerin hanyoyi shida da zakuyi amfani dasu ku hada kudi da wayoyinku.

YouTube


Freelancer


Blogging


Fiverr graphics designer


Fiverr translator


Crypto currency


Wadannan sune jerin abubuwan da zaku yi amfani dasu ku hada tarin kudade dan haka bari muyi dan bayaninsu daya bayan daya.


√ Freelancer

Freelancer wani App ne da zai baka damar dora duk wasu abubuwa naka da kayi wanda zai burge mutane wanda idan mutum ya iya aiki dashi zaisa mutane suna bashi ayyuka domin yayi musu akwai inda zaku dauko wannan app din bayan kun dauko kuma kuyi bincike akansa zaku gane ayyukansa wanda mu bamuyi bayaninsa ba saboda ba lokaci amma dai ana samun kudi dashi sosai dan haka zamu ijiye Link dinsa da a kasa wanda kuna danna gurin da aka rubuta ( nan) to zaku dauko shi.

👉 Nan

√ BloggingWannan harka ce mai matukar sauki kuma wacce take kawo kudi kamar ba gobe domin wannan site din da kuke karanta wannan labarin ma blogging dinne wato website, idan mutum ya bude website nasa kuma yazo da abubuwan da yake dorawa har mutane suke kalla to ina sanar muku zai samu kudi fiye da tunaninku.


√ YouTube channel


Wannan ma hanya ce da ake samun kudi da ita sosai, domin hatta manyan mutane malamai da yan siyasa da yan kasuwa da yan wasan kwallon kafa da yan wasan kwaikwayo yanzu za kuga sun rikewa wannan hanyar wuta domin yadda take kawo kudi dan haka kuyi bincike a Google ko ku tambayi wani da yake harkar zai fada muku yadda ake samun kudi.


√ Fiverr graphics designer


Itama kamar app na farkon ne wanda zai baku damar kuna sayarwa mutane irin ayyukan da kuke da basirarku dan haka shima zan ajiye muku Link din yadda zaku dauko shi.

👉 Nan 

     Nan

√ Fiverr translatorWannan kuma hanya ce da zata baka damar yin amfani da duk kalar yaren da kake so wajen hada sauran ayyukanka.

Danna nan domin daukowa

👉Nan


√ Crypto currency


Wannan kuma babu abinda zance saboda inaga kamar mutane sun san hankar kuma sun san yadda take kuma ba sai an fadi yadda ake samun kudi da ita ba.

Sannan koda searching ne zaku iya yi domin kuga amfanin wadannan apps din dana fada muku wanda ba Apps bane suma kuyi bincike akansu dama su wadannan apps din zasu taimaka ne wajen gina wadannan abubuwan guda biyun blogging da kuma YouTube.


Comments