Min menu

Pages

Wani Attajiri A Jos Ya Yi Rasuwa Mai Ban Mamaki

 Wani Attajiri A Jos Ya Yi Rasuwa Mai Ban MamakiDaga Abba Abubakar Yakubu


Wani fitaccen attajiri a Jos, babban birnin Jihar Filato, mai suna Alhaji Sama'ila Mohammed Mai Bulo ya rasu jiya Litinin da maraice, bayan wata gajeruwar rashin lafiya.


Tun da sanyin safiyar yau Talata dubbannin  jama'a masoya, daga ciki da wajen garin Jos suka hallara a unguwar Rogo, bayan Babbar Tashar Bauchi, domin halartar jana'izar sa.


An daɗe a Jos ba a ga mutumin da rasuwar sa ta girgiza kowa ba, kuma ta ja hankalin jama'a manya da matasa, inda kowa ke yabon kyawawan halayen sa na kyautatawa, jin ƙai, kishin addini da taimakawa mabuƙata.


Tun daga gidan mamacin har zuwa maƙabartar Narkuta haka jama'a suka riƙa takawa da ƙafa, don rakiyar gawar sa, saboda dafifin jama'a da cukoson ababen hawa.


Allah ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe. Shi kuma Allah ya haskaka makwancin sa, Ya sa aljanna ce makomarsa da mu baki daya.

Comments