Min menu

Pages

Rigimar Adam A Zango da Ummi Rahab Allura zata Tonu Garma Ali Artwork ya Tsoma Bakinsa

 

Rigimar Adam A Zango da Ummi Rahab  Allura zata Tonu Garma Ali Artwork ya Tsoma BakinsaBayan wallafa maganar da tayi akan tsohon mai gidanta wanda ya baiwa mutane mamaki nan cewa ya daina bata mata suna ko ta tona masa asiri.


Sai kawai ta wallafa wani dan gajeren bidiyo mai dauke da kalma cewa:

Ummi Rahab: “In ka ji ana yin zancen ka, to ka kai a yo ne!”


Shine shahararren mai shirya barkwancin nan kuma tsohon yaron adam a zango yaje a shafinta yayi wannan rubutu.

“@aliartwork Ki tashi da Addu’a kuma ki rike Allah Ummi Allah zai baki kariya ta hanyar da Baki ta tsammani ba da Yardar Allah”

Sai wani ya ya maryar masa da martani kamar haka.

“@real_sadeek_abdul@aliartwork maimakon kayimata nasiya sabida taraina nagaba da ita yau idan kaine zakaji dadi hakan ba daidai bane gaskiya yakamata idan yara sunyi laifou”

Sai ya shi aliartwork ya sake mayar masa da martani kamar haka.

@aliartwork@real_sadeeq_abdul Ni bana Hassada ko gaba da wanda Allah ya daukaka saboda nasan meye daukaka shi mai daukaka nasiha ake masa a magana ba da zagi ba wannan Yarinyar a girmanta bai kamata tun yanzu a fara Hassada da ita ba akan Allah ya daukakata kamata yayi a mata nasiha ba Goriba kuma daukaka Allah ke bada ta ba mutum ba duk wanda yake daukan cewa shiyake bada daukaka to da Allah kake ja ku dinga cikakken bincike akan abu wanda baku san zahirin me ke faruwa ba dan mutum yafito ya fadi san ransa bai kamata ku dauka ba sai kuyi bincike kada ka zama mai danne hakkin mutum dan kun ganta mace saboda bata da bakin da zata zo ta yi magana na san rai inda kunji ta bakinta killa duk masu zaginta wallahi sai suji kunya dan Allah mu dinga yiwa kan mu Adalci”

Inda kuma aliartwork ya sake cewa : “Allah ya rabaki da Sharrin magauta Ummi”

Wannan ya nuna cewa akwai bayyanai da cikakken bayyani almarin da mutane ke son ji na wannan rabuwar sai a fidda mai gaskiya.

Kuci Gaba Da Bibiyarmu Domin Ci Gaba Da Samun Cikakken Labarin.

Comments