Min menu

Pages

Professor Sheikh Ibrahim Maqari ya janye karan Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon kaya da ya shigar zuwa kotun Musulunci a Kano saboda wannan dalilin

Professor Sheikh Ibrahim Maqari ya janye karan Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon kaya da ya shigar zuwa kotun Musulunci a KanoSheikh Ibrahim Maqari ya fadi dalilan janye karar, inda yace wasu manyan kasa da shugabannin Nigeria har da mahaifinsa sune suka bashi shawaran ya janye karan


Yace cikin wadanda suka bashi shawaran har da wasu manyan jami'in tsaro a wannan Gwamnatin, sun ce zasu kira Malam Abdallah a sirrance ya kawo musu dalilansa akan maganar da yayi wa Malam Ibrahim Maqari, idan bai da hujja zasu bukaci ya rubuta takardan bada hakuri wa Malam Maqari


Malam Maqari yace ba burinsa bane ya tozarta duk wani mutumi da ya jingina kansa da karatun addini, kuma dalilin da yasa ma ya shigar da kara kotu a farko shine don abin ya shafi al'ummah ne, amma tunda manya sun shiga ciki ya janye karan


Alhamdulillah wannan matakin yayi, kuma muna kyautata zaton wannan sabanin zai zama sanadi na haduwar kan Malaman da kuma gyara kuskurensu gaba daya


Muna rokon Allah Ya cigaba da hada kan Musulmin Nigeria a tafarkin gaskiya Amin

Comments