Min menu

Pages

Mutumin nan daya sanyawa yaron da ya haifa kwankwaso sun samu damar ganawa dashi a gidansa dake kano ga abinda suka tattauna..

 Mutumin nan daya sanyawa yaron da ya haifa kwankwaso sun samu damar ganawa dashi a gidansa dake kano ga abinda suka tattauna..

Daga Abdulrahim Yusuf BulanguWannan bawan Allan mai suna Dattijo daya sanyawa yaron daya haifa sunan Dr Rabiu Musa kwankwaso Dan garin Bulangu dake karamar hukumar kafin Hausa jihar Jigawa ya samu damar ganawa da jagoran talakawan wato Dr Rabiu Musa kwankwaso a gidansa dake kano.


Yace shi abinda jagoran yayi musu ne tun shekarar dubu biyu da goma sha hudu yasa yaji duk duniya babu wani dan siyasa mai irin halinsa domin lokacin da suke cikin halin kunci a kudu yayinda aka tsare motocinsu kwankwaso ne yayi silar fitarsu lokacinda ruwan sha ma gagararsu yake wasu saidai su sha fitsarinsu.Dan haka ya kudurta a ransa duk ranar da matarsa ta haifi na miji sunansa zai sanya saboda abinda yayi musu.


To cikin ikon Allah sai kwanannan matar tasa ta haifi na mijin kuma ya sanya masa wannan sunan.Cikin ikon Allah kwankwason yaji duk abinda ya faru kuma yaji dadi daga karshe ma an kira mahaifin yaron zuwa gurin kwankwaso kuma ya nuna jin dadinsa na samun mai suna da akai masa.


Hakika jagora kwankwaso mutum ne mai nagarta kuma mai kokari samun kamarsa sai an dage

Comments