Min menu

Pages

Nafi Sha'awar Fitowa 'Mugu' A Cikin Fim, - Adam A. Zango

 Nafi Sha'awar Fitowa 'Mugu' A Cikin Fim, - Adam A. ZangoFitaccen Jarumi kuma Mawaki a Masana'antar Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana cewa, yafi shawa'awar fitowa a matsayin Mugu a cikin shirin finan-finan Hausa.


Adam A. Zango ya bayyana hakane acikin shirin 'Daga Bakin Mai Ita' na BBC Hausa.


Jarumin ya bayyana cewa dalilinsa na son fitowa a matsayin Mugu shine aktin ne wanda ba kowa zai iya yin sa ba, idan aka kwantata shi da aktin din soyayya wanda kusan kowa zai iya.


Adam A. Zango ya kuma bayyana Marigayi Rabilu Musa Ibro da Shu'aibu Kumurci a matsayin jaruman da suka fi burge shi a Masana'antar Kannywood.Comments