Min menu

Pages

Kamin Ki Amince Da Soyayyan Namiji Kiyi Nazarin Wadannan Abubuwan

 Kamin Ki Amince Da Soyayyan Namiji Kiyi Nazarin Wadannan Abubuwan:

 


Wasu 'yan matan da zaka Kwana kana tambayrsu me yasa suke son wanda suke soyayya da shi a yanzu haka. Amsar da wasu zasu baka yana cike da takaice kwarai da gaske.


Kada ki sake ki soma soyayya da namiji har sai kin yi nazarin wadannan abubuwan kamar haka:


1: Shi wannan da yake sonki yana cikin irin mazan da kike fatan ki aura. Wannan shine abu na farko da duk wata budurwa zata soma yiwa kanta tambayar kamin ta soma soyayya da mai sonta da aure.


2: Kin shirya yin irin soyayyar da wannan namijin yake son yayi dake?


Wasu mazan zasu zo ne da nufin suna son su aureki, nan gaba ko kuma nan bada jimawa ba.


Wasu kuwa zasu ce miki basu da niyar yin aure yanzu ko nan gaba. Wasu kuwa karara zasu fadamiki zina suke bukatarki da shi. Shin kin shirya yin irin wannan soyayar daya bukata daga gareshi. Idan kika samu amsar wannan tambayar daga nan sai ki zabi nayi.


3: Ki tabbatar kamin baiwa namiji damar soma soyayya dake kin daura shi akan sikeki da minzanin da kike so tabbatar da cewa ya dace a dabi'ance ya zama masoyinki.


4: Idan kin bashi hadin kai zai iya kula da bukata tunki kamin aure da bayan aure.


Wannan yana da mahimmanci domin shi soyayya musamman na aure yana cike da yiwa mace hudima kamin da bayan aure.


5: Kin gamsu da soyayyar da yake miki bana zai disashe a karamin lokaci ba.


Wasu masoyan suna haba haba da mace ce kamin sun samu biyan nasu bukata na aure ko na akasin hakan.

 

Wannan sune wasu daga abubuwan da duk wata budurwa zata yi Nazarinsu kamin baiwa saurayi daman soyayya da ita.


Allah Yaku maza na gari

Comments