Min menu

Pages

Zan iya Mutuwa akan Rashin Lafiyar dake damuna in ba ai saurin kaini asibiti ba>>Nnamdi Kanu ya shaidawa Kotu

 Zan iya Mutuwa akan Rashin Lafiyar dake damuna in ba ai saurin kaini asibiti ba>>Nnamdi Kanu ya shaidawa Kotu




Shugaban Rajin Kafa Kasar Biafra Nnamdi Kanu yayi karar Gwamnatin Najeriya, akan cigaba da tsare shi da akeyi a Shalkwatar Rundunar tsaro ta Farin Kaya.


A watan yuni, aka kama Shugaban Rajin Kafa kasar Biafra a Kasar Kenya, tare da maido dashi kasar Najeriya.


Inda daganan, aka gabatar dashi a Gaban Babban Jojin Babbar Kotu ta Abuja, Binta Nyako, inda ta bukaci a cigaba da tsare shi a Shalkwatar Rundunar tsaro.


Kanu na fuskantar zarge-zarge, ciki harda cin amanar Kasa sakamakon Gwagwarmayar shi na Kafa Biafra.


An dai bayar dashi beli a watan Afrilu na Shekarar 2017 akan rashin lafiya, amma ya kyale belin, bayan an bashi akan sharudda.


A karar daya shigar a Babbar Kotu dake Abuja ta hanyar lauyan shi Ifeanyi Ejiofor, Shugaban Kungiyar IPOB ya bukaci Kotun data mai dashi daga Shalkwatar Hukumar tsaro ta Farin Kaya zuwa Cibiyar Gyaran Akida dake Kuje, Abuja, kafin a badashi beli.


Lauyanshi Wanda ya bukaci Kotu data bayar da dama Likitocinsa su rika duba lafiyar sa, amma a cikin inda yake a tsare.


Kanu ya kara dacewa, zai iya mutuwa, idan rashin lafiyar sa ba'a duba shi yadda ya kamata.

Comments