Min menu

Pages

Za A Gurfanar Da Abduljabar A Kotu Kan Zargin Batanci Ga Manzon Allah

 Za A Gurfanar Da Abduljabar A Kotu Kan Zargin Batanci Ga Manzon Allah




Bayan kammala mukabala a ranar Asabar tsakanin Malam Abduljabar Nasiru Kabara da zauren hadin kai na Malaman Kano, inda aka yi dogon zama domin jon bahasin Abduljabar kan kalaman batanci da ake zargin yana yi ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, tambayoyin da ya kasa bada amsa a cewar Alkalin zaman.


Majiya mai tushe ta tabbatar da cewar an kammala shirye shiryen gabatar da Malam Abduljabar a gaban kotu domin tuhumarsa da kalaman batanci ga janibin Annabin Allah mai tsira da Amincin Allah.


Tuni dai rundunar 'yansanda ta jihar Kano ta gayyaci Abduljabar da ya bayyana a gabanta ranar Litinin domin amsa tambayoyi tare da gabatar da shi gaban Shariah, kamar yadda kakakin Rundunar'yansanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Manema labarai cewar sun gayyaci Abduljabar tun ranar Juma'a, amma saboda wannan mukabalar suka daga gayyatar zuwa ranar Litinin.


A yayin wannan mukabala dai, shugaban zaman kuma Alkalin mukabalar Farfesa Salisu Shehu ya bayyana cewar, Abduljabar Nasiru Kabara ya gaza bada amsar dukkan tambayoyin da akai masa, dan haka yake shawartar Gwamnatin Kano da ta dauki mataki kan Malamin tunda baya bada hadin kai a tambyoyin da ake masa.


Abduljabar Nasiru Kabara yana yin wasu kalamai marasa dadi ga fiyayyen halitta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam inda yake ikirarin maganganu sun zo a cikin litattafan Buhari da Muslim, inda aka nemi ya nuna gurin da yake ikirari a cikin littafin, amma ya kasa nunawa.



Comments