Min menu

Pages

Wata Rana Za A Zo Ana Yabon Buhari – Zainab Shamsuna Ahmed

 Wata Rana Za A Zo Ana Yabon Buhari – Zainab Shamsuna Ahmed



Ministar kudi da tsare-tsare a Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta mayar da martini ga wadanda suke korafin cewa Najeriya na yawan ciye-ciyen bashi.


A wata hira ta musamman da ta yi da Muryar Amurka, ministar ta ce bashin dalar Amurka biliyan 35 da Najeriyar ta ciyo ba abin damuwa ba ne, tana mai cewa wasu basussukan ma gadon su gwamnatin ta APC ta yi.


“Dole ce take sa muke daukan wannan bashi, ba wai ana dauka kawai don muna son daukan bashi ba. Dole ne mu gina layin dogo, dole ne mu gyara filin tashin jirage, dole ne mu gina manyan hanyoyi da ake bukata. Idan ba a yi haka ba, to za mu ci gaba da komawa baya.” Ministar ta ce.


A cewarta, idan gwamnati ta ce za ta tsaya ta tara kudi daga cikin gida kafin ta yi wadannan ayyuka, “to za mu koma can baya, saboda haka, dole ne ya sa ake haka.


“Nan gaba wata rana mutane za su ce lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jarumta, ya fahimci abin da ya kamata ya yi a lokacin, idan ba mu yi hakan yanzu ba daga baya za a zo ana da na sani.”


A ‘yan kwanakin nan an yi ta tafka muharawa a Najeriya musamman daga bangaren ‘yan adawa kan cewa gwamnatin ta Buhari tana cin bashin da ya wuce kima, inda har babbar jam’iyyar mai mulki ta PDP ta yi kira ga gwamnatin da ta yi hattara.

An samu wasu suna korafin cewa, matakan da gwamnati take dauka na ciyo basussuka, zai bar al’umar dake tafe da dumbin basussuka, sai dai Shamsuna Ahmed ta kore wannan korafi.


“Mu da muka zo, mu ma akwai basussukan da muka samu, kuma muna nan muna kan biya. Har yau ba mu fasa biyan bashi ba, kuma bashin nan na shekara da shekaru ne na gida da na waje da muka samu.”


“Haka mu ma idan muka gama aiki, haka wani zai ko wata za ta zo ta ci gaba da biya.” In ji minister kudin

Comments