Min menu

Pages

ALLAHU AKBAR:- DAN BALL DIN LIVERPOOL SADIO MANE YA FADI WATA MAGANA MAI TABA ZUCIYA

ALLAHU AKBAR:- DAN BALL DIN LIVERPOOL SADIO MANE YA FADI WATA MAGANA MAI TABA ZUCIYASadio mane dai dan kwallo ne dake buga wasa a club din Liverpool sannan dan kasar Senegal ne, ya fadi wata magana wacce ta taba zuciya inda yace


Ni ban maida hankali na sosai akan sai na sayi kaya masu tsada ba, kamar manyan motoci da kuma manyan wayoyi.

Ni babban burina bai wuce naga mutanen dana baro suna zaune cikin amunci ba, suci su sha su kwanta a guri mai kyau, sannan su samu asibiti da masallaci dadai sauran abubuwan da zai taimaka musu.


Bazan iya zama na huta ba dole sai na tabbatar mutanen dana baro sun samu wadannan abubuwan..

Domin ni gurin dana baro gurine da suke da bukatar abubuwan kamar makarantu da kuma asibitoci..


Duk da haka ina yiwa yan uwana yan kwallo farin ciki idan na gansu da manyan motoci da kuma gurin rayuwa mai inganci domin kowa nada nasa ra'ayin, amma ni a yanzu babu batun sayan wadannan kayayyaki a gareni bayan nasan gurin da nake nada matukar bukata.


Bukata ta bata wuce naga mutanena suma suna cikin kwanciyar hankali da rufin asiri ba.

Comments