Min menu

Pages

Ku bar mazajenku su kara aure, inda hali ma ku taimaka musu da kudi domin su auro wasu matan inji wata budurwa

 Ku bar mazajenku su kara aure, inda hali ma ku taimaka musu da kudi domin su auro wasu matan inji wata budurwa
Wata mata ta shawarci ’yan uwa mata da su dafawa mazajensu idan za su kara aure


Wata mata ta nemi mata su tallafawa mazajensu idan sun gabatar da bukatar kara auren mace ta biyu


Ta ce kada mata su yi fada da junansu saboda maza


Maza a shafukan sada zumunta sun yarda da ra'ayinta


Wata mace Musulma 'yar kasar Kenya ta bukaci mata da su tallafa wa mazajensu idan sun yanke shawarar auren mace ta biyu.


Matar tana magana ne da 'yan uwanta mata ta hanyar bidiyon TikTok wanda aka yada ta mai amfani da sunan @nps254 kuma tun daga lokacin bidiyon ya karade shafukan intanet.


Ta ce mata su daina fada da maza saboda auren mace fiye da daya abu ne na al'ada.


Tace Idan iyayensa ba su yi fada a kansa ba, to ku a wa za ku yi fada a kansa, namiji mai aure? Don haka lokacin da mutum ya yanke shawarar yana son kara aure, kawai yi masa addu'ar ya samu mata ta gari wacce za ku taimaki juna.


Matar 'yar kasar ta Kenya da ba a san ko wacce ce ba, ta ce lokaci ya yi da mata za su daina fada da juna a kan maza kuma maimakon haka su karkata zuwa fada a kan ilimi da aiki da samun karin girma da ci gaba da ma sauran ababuwa masu kyau.


Takara da cewa "Auren mace fiye da daya yana nan, ko mun yarda da shi ko mun ki shi ko mun musanta shi. Amma fa yana nan daram. Ko mazajen Kirista ma ya kamata su daina boyewa suna komawa gida wurin matansu, amma a gefe suna da farkar da suka boye a wani wurin. Wannan ba shi ne mafita ba. Ku gabatar da su kuma ku sanar musu da junansu.


Galibin mazan da suka yi tsokaci sunyi na’am da ra'ayinta inda suka nemi matan da su daina nuku-nuku a kan batun auren mace fiye da daya muddin dai mijin nasu yana adalci tsakaninsu.


Sai dai wadansu mata sun dage cewa aure ya kasance tsakanin namiji daya da mace guda kawai kuma auren mace fiye da daya yana jagula zamantakewar iyali.Comments