Min menu

Pages

Kotu ta bayar da belin tsohon magatakardar JAMB akan N200m

 Kotu ta bayar da belin tsohon magatakardar JAMB akan N200m




Babban Jojin Babbar Kotu ta kasa dake Abuja, Mai Shari'a Obiara Egwuatu, a ranar Alhamis ya bayar da belin Tsohon Magatakardan Hukumar Tsara Jarabawar Share Fagen Shiga Jami'a wato-JAMB, Farfesa Adedibu Ojerinde, akan belin Naira Miliyan 200 a Shari'ar da ake zarginsa na karakatar da kudaden Gwamnati.


Mai Shari'a Egwuatu a hukuncin daya yanke akan Neman bayar da belin Ojerinde, yace babu wata hujja Daya samu wadda zata hana bayar da belin Wanda ake zargin.


Ya kuma umaci Wanda ake karar daya kawo mutane guda biyu masu shaidar biyan Haraji, Wanda suke zama a Abuja, da zasu tsaya mashi a bayar da belin nasa.


Daya daga cikin mutanen da zai kawo a matsayin shaida, sai ya kasance Farfesa a Jami'ar Gwamnatin Tarayya, daya Kuma saiya kasance yana da kaddara a Abuja, Wanda Kuma sai Kotu ta tantance shi.


Haka Zalika, Farfesan sai ya kawo takardu da zasy tabbatar da zaman shi a matsayin Farfesa, takardar daukar aiki da I.D Card.


Mai Shari'a Egwuatu ya dage Shari'ar ya zuwa 22 da 23 ga watan Juli domin cigaba da Shari'ar.


Hukumar kula da masu Zagon Kasa mai zaman Kanta wato-ICPC ta kama tsohon Magatakardan Hukumar JAMB akan zarge-zarge guda 18 da suka hada da karkatar da Dukiyar Gwamnati da kudaden yakai Naira Miliyan 900.


Rahotan da Jaridar Dimokradiyya ta samu, ya nuna cewa ya karkatar da kudaden ne a lokacin da yake Jagorantar Hukumar JAMB.

Comments