Min menu

Pages

Gwamnonin kudu sun gargadi Buhari cewa basu yarda a sake kama wani nasu ba

Gwamnonin kudu sun gargadi Buhari cewa basu yarda a sake kama wani nasu baBamu Yadda A Sake Kama Wani Daga Yankinmu Ba, Dole Saida Izininmu, Gwamnonin Yankin Kudu Sun Gargadi Shugaba Buhari Gwamnonin yankin kudancin Nijeriya sun bayyana sabon tsarin aiki ga gwamnatin Nijeriya. 


Sun ce, ba su amince a sake kame wani ko gudanar da wani aiki ba tare da an nemi izini daga gwamnan jiha ba.


Haka zalika sun nuna rashin jin dadinsu da yadda jami'an tsaro ke kame jama'ar yankin ba tare da la'akari da hakkin dan adam ba.


Wannan gargadin nasu na zuwane bayan gwamnatin Nijeriya ta kama shugaban tsagerun kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, da kuma kokarin kamo shugaban tsagerun kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho da take yi.


Shin me zakuce game da wannan gargadin?

Comments