Min menu

Pages

Zazzafan gargadi zuwa ga yan Nijeriya tare da Sheikh Ahmad Gumi

 GARGADI zuwaga Sheikh Ahmad Mahmud Gumi:Ku zagaya da wannan yaje kunnen yan nigeria:


Rundunar Sojojin Nigeria na gargadi ga sheikh Ahmad Mahmud Gumi da yafitar da kanshi tsakanin sojoji da yan ta’adda a nigeria.


Muna girmama addini da malaman addinin muslunci kasancewar mu musulmi ne. Malaman addini suna da girma da daraja a idon rundunar sojoji da gwamnatin nigeria bakidaya.


Saboda haka muna kira ga malam Ahmad Mahmud Gumi da yafitar da kanshi akan lamarin tsaron nigeria. Domin bamaso a walakanta malamin musulunci a karkashin wannan tafiyar tamu.


Gwamnati bata tura malam ba domin yaje yanemi sulhu da yan ta’adda 


Rundunar sojojin Nigeria bata tura malam ba domin yaje yanemi sulhu da yan ta’adda bah


Ba jami’an tsaron basuka tura malam wurin sulhu da yan ta’adda bah


Al’ummar Nigeria basu tura malam yaje neman sulhu da yan ta’adda bah


Saboda haka malam yana kalaman tunzurar da yan ta’adda dasuke karawa yan ta’adda karfin gwuiwa wurin kara kai hare hare a kauyuka.


Saboda haka muna gargadin malam da yafita hanyar da yakama idan bahaka bah za’a hukunta shi kamar yanda doka ta tanada.

Comments