Min menu

Pages

Yanzu-yanzu Kamfanin Twitter ya yi Allah-wadai da matakin da Buhari ya dauka kan su

Yanzu-yanzu Kamfanin Twitter ya yi Allah-wadai da matakin da Buhari ya dauka kan suYanzu-yanzu jami'ar yada labarai ta kamfani Twitter a Turai da gabas ta tsakiya da kuma Africa ta bayyana rashin jin dadin su akan matakin da shugaba Buhari na Najeriya ya dauka kan su, na dakatar da yin amfani da Twitter a duk fadin Najeriya a yau Assabar.


Jami'ar ta bayyana cewa yanzu haka kamfanin yana bincike kuma zai fitar da sakamakon binciken da ya gudanar a nan gaba kadan akan wannan lamari.


A jiya juma'a ne dai fadar shugaban kasar Najeriya ta bada umurnin dakatar da yin amfani da Twitter a duk fadin Najeriya.


Hakama, Najeriya itace kasar da ta fi kowace kasa kawo ma kamfanin na Twitter kudade a duk nahiyar Africa.


Comments