Min menu

Pages

WATA SABUWA: Akwai yiyuwar yau za a yi fitina tsakanin Joe Biden da Putin

 WATA SABUWA: Akwai yiyuwar yau za a yi fitina tsakanin Joe Biden da PutinJoe Bien da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su gana a birnin Geneva na Switzerland a yau, a karon farko tun da Mista Biden ya zama shugaban Amurka.


Sai dai masu sharhi na ganin da wahala a kwashe lafiya a tattaunawar.


Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta dade da yin tsami saboda Amurka na zargin Rasha da kitsa hare-hare ta intanet da kuma katsalandan a zaɓukanta na 2020.


Tana kuma zargin Rasha da take hakkin bil Adama ciki har da tsare jagoran 'yan adawa Alexei Navalny.


Sai dai babu alamun Mista Putin zai taba sauya manufofinsa na maida kasashen yammacin duniya saniyar ware ta fuskar gudanar da ayyukansa.

Comments