Min menu

Pages

Wata mata ta haifi jarirai goma lokaci guda

 Wata mata ta haifi jarirai goma lokaci gudaMasu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, Ikon Allah sai kallo. Kwarai kuwa, domin idan kaji ko kikaji labarin wannan mata yar ƙasar Afirka ta kudu, dole ka jinjina, ka kaɗa kai gamida shiga tunani, na mamakin kasantuwar faruwar wannan abin al’ajabi haka.

Ita dai wannan matar, ta zama mace ta farko a tarihi bawai a ƙasar Afirka ta Kudu ba, harma a duniya gabaki daya kwata, inda ta fara haifo yara guda goma rigis batare da samun ko wani irin tasgaro ba.

Matar mai suna, Gosiame Tamara Sithole dai tana da shekarun haihuwa talatin da bakwai ne a duniya, kuma ta goge tarihin wata mata ne data fito daga ƙasar Senegal mai suna Halima Cisse , inda ita Haliman ta haifi ya’ya tara rigis a watan jiya na Mayu daya gabata

A daren jiya na litinin ne, Mrs Gosiame Tamara Sithole ta haifi ƴaƴa goman a wani asibiti da yake a birnin Pretoria.

Comments