Min menu

Pages

WANI MUTUM YA GINA GIDAN MILIYAN DUBU KWANA 2 DA TAREWA YA MUTU

WANI MUTUM YA GINA GIDAN MILIYAN DUBU KWANA 2 DA TAREWA YA MUTU:Malamin addinin musuluncinnan mai suna malam Abdulrasheed a cikin karatunsa ya bada wani labari mai tsoratarwa da sosa zukatan mutane musamman masu burin tara abin duniya wadanda basu da wani burin da ya wuce su tara dukiya mai yawa.


A cikin labarin malamin yana cewa, "Akwai wani bawan Allah mai kudin gaske wanda ya gina wani katafaren gida na alfarma gida na azo a gani, tunda ya gina gidan duk kayan alatun da aka saka a cikin gidan babu abinda aka siya a Najeriya, domin kuwa duk illahirin kayan darururwan miliyoyin da aka zuba a gidan.


Anyo saffararsu ne daga kasashen waje irin su Ingila Dubai da sauransu, amma abin al'ajabi da ban tausayi a labarin wannan bawan Allah shine, ya gama gina gidan ya tare ciki da iyalansa kwanan shi biyu kacal ya hau mota daga Kaduna zuwa Abuja, yayi hatsari ya mutu.


Lokacin da aka kawo gawar sa a cikin gidansa ana kokarin shigar da ita cikin falo, sai iyalansa suka ce kar a shigar musu da gawarsa, a ajiye shi can gefen dakin baki a waje ayi masa wanka aje a rufe shi saboda kar a shigar musu da shi cikin falo ya bata musu falon da jini, alhali shi yayi wahalar nemo kudin da ya gina gidansa.


Wanda a kiyasi ya kai kusan Naira million duba, to kunga duniya kenan saboda haka muyi kokari mu gyara alakarmu da Allah mu gina gidan mu na lahira saboda shine tabbas kuma dauwamamme amma na duniya aikin banza ne kuma matsugunni ne, muna fatan Allah yasa mu gyara ameen da fatan za kuyi shared zuwa sauran groups don yan uwa su amfana.

Comments