Min menu

Pages

AN SOKE AL'ADAR SIGN OUT DA DALIBAI SUKE YI A MAKARANTA

 An soke sign Out a makarantu a wata makarantaShahararriyar jami’ar nan ta Umaru Musa Yar’adua University Of Katsina wato UMYUK a takaice ta sanar da soke al’adar nan ta sign out wacce dalibai ke yi a duk lokacin da suka zana jarabawarsu ta karshe wace final exam inda za kaga samari da yan mata suna sanya fararen riguna.Ko Ti shart da zarar sun fito daga dakin zana jarabawar sai maza da mata su cakudu a guri guda kowa dauke da abun rubutu wato maka, yana zana sa hannunsa wato signature a turance, a jikin rigar dalibi ko daliba.


A jiya ne dai hukumar gudanarwar jami’ar ta UMYUK ta fitar da sanarwar haramta wannan al’ada ga illahirin daliban jami’ar, sai dai tuni a nasu bangare daliban makarantar suka soma mayar da martani kan wannan haramci inda wasu ke cewa hakan yayi dai dai yayin da wasu ke ganin ba’a kyauta musu ba.


Kunji fa menene ra’ayoyinku shin kuna goyon bayan daukar wannan mataki?

Comments