Min menu

Pages

Wani mutum ya gaurawa shugaban kasar faransa Mari

 Wani mutum ya gaurawa shugaban kasar faransa Mari Wani mutum ya gaura wa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a lokacin ziyarar da yake yi a kudu maso gabashin kasar.


A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Mr Macron yana tafiya zuwa wajen wani shinge lokacin balaguron da ya yi zuwa Tain-l'Hermitage da ke wajen birnin Valence.


Mutumin ya wanke Mr Macron da mari a fuska ne kafin jami'ai su yi hanzarin kai masa dauki. Daga nan ne aka janye shugaban.

Kafofin watsa labaran Faransa sun ce an kama mutum biyu bayan gaura wa shugaban kasar mari.


Saidai lokacin da mutumin yai marin anji mutane nayin ihun suna tofin Allah tsine..

Comments