Min menu

Pages

Muna Binkicen Tinubu, Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa: Muna binciken Tinubu ~ Shugaban EFCC

 Muna Binkicen Tinubu, Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa: Muna binciken Tinubu ~ Shugaban EFCCShugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu'annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce wani tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, yana kan bincike.


Ya ce: “Kun yi min tambaya a baya game da kame mutane kafin bincike kuma yanzu kuna cewa me ya sa ba mu kama Tinubu ba?


“Ana ci gaba da bincike, Lokacin da kake bincika lamura irin haka, ba kasafai ake gama su a rana guda ba. Dan haka mu a wajen mu Dubban bincike na ci gaba, a kowace rana.


"Kun fahimta? Duk da cewa kun fito ne daga kafofin watsa labarai. Kada ku ce muna koya muku aiki amma dai ba ko wana abu muke faɗi a kafofin sadarwa ba.


An ce ka nemi fom din bayyana kadarorin Tinubu lokacin da kake shugaban Ofishin shiyya na Legas? Eh, haka ne. Dan haka ma yasa muka ƙara dagewa yanzu da na samu matsayin Shugaba.

Comments