Min menu

Pages

Me yai zafi:- Yan Kungiyar IPOB Sun Fille Wa Bokansu Kai

 Me yai zafi:- Yan Kungiyar IPOB Sun Fille Wa Bokansu Kai 


Jerin sarakunan da sukafi tarin dukiya a Africa

'Yan Kungiyar Ta'adda ta IPOB masu neman a raba kasa sun yanke wa bokansu mai suna Paschal Okeke dan garin Umudim-Ukwu Orji da ke karamar hukumar Oru ta Jihar Imo kai don zargin da suke masa cewa maganin da ya ba su na kare kai bai yi aiki ba.


Mai ba wa Kwamishinan 'yan sanda Imo shawarar kan harkar jaridu, Mike Abattam ne ya ba da wannan sanarwar. 


Sanarwar ta ce 'yan kungiyar ta'addan su harbi shi da bindiga a wajaje da dama, kafin su fille masa kai sannan su kona gidansa.


A cewarsu suna zargin shi da ba su layoyi da bai yi aiki ba wanda hakan ya sa hukumar tsaro ta kama tare da karkashe masu mayaka da dama a Jihar.

Sauran da suka tsira ne su koma suka huce haushinsu a kan bokan nasu wanda daga bisani suka yi guduwa-gunduwa da jikinsa sannan suka kona shi kurumus

Comments