Min menu

Pages

ALHERIN ALLAH YA KAIWA CHRISTIANO RONALDO

 ALHERIN ALLAH YA KAIWA CHRISTIANO RONALDOShahararren 'dan wasan kwallo na duniya Christiano Ronaldo ya ture kwalaben Coca-Cola guda biyu na haramtacciyar Kasar Isra'ila daga gabansa domin bayyana bakin cikinsa akan ta'addancin da Isra'ila take yiwa Falasdinawa


Coca-Cola da Pepsi duka mallakin Kasar Isra'ila ne, duk wanda ya cire kudinsa ya sayi Coca-Cola ko Pepsi to ya taimaka da wani kaso na kudi kai tsaye zuwa ga asusun ajiyar kudi na haramtacciyar Kasar Isra'ila wanda take amfani da kudaden wajen daukar nauyin ta'addancin da take yiwa Falasdinawa


Na daga cikin dalilan da ya sa Ronaldo ya ture kwalaban Coca-cola guda biyu da aka ajiye a gabansa gurin wani taro  domin ya bayyana fushinsa akan ta'addancin da Isra'ila take yiwa Falasdinawa


Christiano Ronaldo ba Musulmi bane,  amma  yayi fice wajen nuna goyon bayansa ga 'yan uwa Musulmi Falasdinawa, yana fitar da dukiyarsa wajen taimakon Falasdinawa tare da daukar nauyin karatun yaran Falasdinawa da Isra'ila ta kashe iyayensu


Muna rokon Allah Ya yiwa Christiano Ronaldo tukwici da karban addinin Musulunci Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Comments