Min menu

Pages

Zaku zama makafi matukar baku daina aikata wadannan abubuwan ba musamman na uku a cikinsu

 Zaku zama makafi matukar baku daina aikata wadannan abubuwan ba musamman na uku a cikinsu.Da wuri idanuwanku zasu lalace zaku samu matasala ta daina gani idan baku gujewa aikata wadannan abubuwan da zan zayyano muku ba.


Ido abu ne mai matukar girma tare da amfani ga kowacce halitta mutum ko aljan harma da sauran tsintsaye da kwari, dan haka ake so koda yaushe ya zama muna kare shi da kuma daina aikata ayyukan da lafiyarsu zata tabu.


Domin yanzu idan aka ce mutum baya gani tamkar ya zama wani abu ne abin tausayi domin duk wasu abubuwa mutum bazai samu damar aikatawa ba shi kadai saida dan jagora.


Dan haka muka zo muku da wasu abubuwa wanda in har kuna aikatawa to da wuri idanuwanku zasu makance inji mutanen da sukai bincike.


√ Amfani da Glass ko medical wanda ba'a saita shi daidai da idanun mutum ba wannan yin amfani dashi kan kashe idanu da wuri.


√ Yawan kallon rana shima bincike ya nuna yana daga cikin abubuwan da suke saurin lalata ido dan haka ba'a so mutum yana yawan kurawa rana ido.


√ Kallon bidiyo da photuna na batsa wannan kusan yafi kowanne abu illa ga ido domin matukar mutum zaici gaba da yin irin wadannan abubuwan to da wuri idanunsa zai makance.


√ Shan taba itama masu bincike sunce yawan shan taba kan taka rawar gani wajen lalata ido dan haka sai a kiyaye.Comments