Min menu

Pages

WATA AL'ADA: Dole Goggon Amarya Ta Yi Jima'i Da Ango Dan A Gwada Ƙarfin Sa ga yadda abin yake

 WATA AL'ADA: Dole Goggon Amarya Ta Yi Jima'i Da Ango Dan A Gwada Ƙarfin Sa
Wata Al'adar da wasu mutane ke yi yayin da A ka ɗaura Auren Budurwa a yankin su ta bukatar gwajin budurci daga amarya da kuma karfin iyawa daga ango wanda za a gwada shi da goggon amarya. 


Matan da ke Banyakole a ƙasar Uganda suna da wata Al'ada wacce idan za a miki Aure tilas ne goggon ki ta zama miki babbar ƙawa saboda ƙauna da Soyayya da kuma jagorantar 'yar uwarta ta hanyar zama aminiya ga ƴar yayarta musamman kan abubuwan da ba za ta iya rabawa da mahaifiyarta ba.


Domin a wajen ƙabilar Banyakole na Uganda, aikin inna ya wuce yin nasiha kawai har ma da ɗaukar duk wani nauyi da ya gagari Amarya ta yi shi tare da mahaifiyar ta a al'adance. 


Mutanen Banyakole wadanda kuma ake kira da kabilar Ankole mazauna Masarautar Bantu ce wacce ta samo asali tun daga karni na 15.  Tana cikin Kudu maso Yammacin Uganda, gabas da Tafkin Edward, masarautar da Sarki Mugabe ke mulki wacce ta shahara da kare haƙƙin aure na musamman.


 Auren Banyakole


Aure a cikin wannan al'ada yana da mahimmancin gaske yayin da iyaye ke samun farin ciki da alfahari daga auren 'ya'yansu.  A bisa al'adar Banyakole, idan yarinya ta kai shekara takwas ko tara, aikin inna ne ta gyara ta don rayuwar iyali. Goggon ta za ta koya mata duk wani abu daya kamata ta sani game da matsayinta na mace mafi mahimmanci, a matsayin matar aure.


Budurci a cikin wannan al'ada ana girmama shi sosai don haka dole ne 'yan mata su kaurace wa yin jima'i kafin aure.  Kuma idan aka gano yarinya ba budurwa ba ce kafin aure, to za ta fuskanci hukuncin kisa ko yanke mata hukunci daga al’umma.


Bugu da ƙari, mutanen Ankole suna ɗaukar wasu hanyoyi na gyara budurcin Yaran su Don haka lokacin da ‘yan mata suka kai shekaru takwas ko tara, ana bukatar su riƙa yin kitso inda ake ciyar da su gero, naman shanu, da madara.  Ana yin wannan galibi don 'yan mata ko sa sami damar jawo hankalin miji.


Auren Banyakole ya ƙunshi shagulgula da dama ciki har da lokacin Bayar da kyauta da aka sani da "Kuhingira" inda dangi da abokan amarya ke gabatar mata da kyaututtuka kamar shanu da sauran kayan abinci da za su kai gidanta na aure. Inda bayan kwanaki 10, ana aiwatar da wata al'ada wacce ake kira Okukoza Omunuriro. A nan ne za a sanya Amarya ta ɗora girki ta kunna wutar girkin ta na farko a sabon gidan Mijinta.


A ranar daurin aure, ana shirya biki a gidan amarya inda mahaifin zai yanka bijimi yayin da a gidan ango kuma akwai wani biki na kara aure.  Amma da farko, dole ne a yi bikin gargajiya na karshe, bikin da ya kunshi gwaje-gwaje biyu wanda dole ne goggon amarya ta gudanar da shi.


Tunda budurci shine ma'aunin aure ga matan ƙabilar Banyakole, dole ne kowace amarya a gwada ta da innarta don tabbatar da budurcinta kafin auren. Idan amarya ta wuce gwajin budurci, ana zaton ba ta da ilimin jima’i ko yadda za ta faranta wa sabon mijinta rai ta hanyar jima’i.


Don haka, gwaji na biyu ya shafi goggon amarya tana gwada ƙarfin jima'in da ango ke da shi ta hanyar yin lalata da shi.  A yayin wannan aikin da ake yi a gaban Amarya tana kuma koyon duk dabarun Jima'i da kuma sifofin da aka fi so don ta iya ba wa mijinta gamsuwar da ake buƙata a matsayin ta na Amarya don faranta wa mijinta rai a cikin auren.

Comments