Min menu

Pages

Wallahi Idan ban yi "Wuff" da Bill Gates ba akwai matsala, ku taimakeni: Cewar Mufeeda

 


Wallahi Idan ban yi "Wuff" da Bill Gates ba akwai matsala, ku taimakeni: Cewar Mufeeda


Wata Matashiya a Najeriya Mai Suna Mufeeda Rasheed Galadanchi ta bayyana aniyarta ta yin "wuff" da attajirin nan na duniya Bill Gates.


Shi dai Mista Gates a wannan mako ne ya yi bankwana da mai dakinsa Melinda Gates bayan shafe shekara 27 da bakwai ana soyewa a matsayin ma'aurata.


Tsawon wannan shekaru da Ma'auratan wato Bill da Melinda Gates suka shafe dai, Allah Ya azurta su da samun ya'ya uku a iya rayuwar tasu.


To sai dai Jim kadan bayan samun labarin mutuwar auren tasu ne, Mufeeda ta bayyana muradin ta na yin wuff da Bill Gates bayan kasancewar shi bazauri a halin da ake ciki.


Cikin wani sako da ta aike wa Mista Gates a shafin Instagram, Matashiyar ta bayyana mishi cewa duk da Allah Ya hukunta ba shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a duniya ba, amma hakan ba shine zai hanata zama dakin da Melinda ta fita ta bari ba.


Kazalika baya ga wannan sako da ta aike mishi, ta kuma hada hoton shi da nata a shafin na Instagram inda mabiyan ta da dama suka yi ta sharhi kama daga masu son barka har zuwa masu kushe lamarin.


Ita dai Mufeeda Rasheed Galadanchi, matashiya xe da ta yi suna a shafin sada zumunta na Instagram musamman wurin barkwanci da kuma neman taimako ga wadanda ke da bukata.


Kawo yanzu dai ba a ga martanin Mista Gates ga natashiyar ba, amma ko ma menene, lokaci zai nuna.

Comments