Min menu

Pages

Shin kunsan kabilar da maza ke lakadawa mata duka kafin su aure su?

 Shin kunsan kabilar da maza ke dukan mata kafin su aure su?



Kabilar Hamar Kabila ce mai dadadden tarihi a Kasar Habasha (Ethiopia), wacce take rayuwar ta cikin tsaunuka.


Mafiya akasarin al'ummar ta na zaune ne a yankin Omo Valley dake Kudancin kasar ta Habasha, wanda kuma sun yi amanna da kiwon shanu, domin wani lokacin da ka taɓa musu saniya gwara ka tattara su ka yi gaba da su.


Wannan Kabila ta kware wurin riko da al'adar, to sai dai abin mamaki shine yadda mata ke rokon mazajen da za su aura su lakada musu dan banzar duka.


Hikimar yin hakan a cewar su shine, halan zai tabbatar da tsantsan soyayya da mace ke yi wa namijin, yayin da a ɓangaren namijin kuwa za a iya kiran shi da gwarzon.


Karin al'ajabi a nan shine yadda za a yi wannan dan karen duka a bainar nassi, ta inda kowa zai tabbatar da abin da ya faru, domin na zamowa ne a matsayin sadaki na biyu.



Comments